An Kama Sakataren APC Na Mazaba A Yobe Kan Zargin Aikata Kisan Kai

Rundunar ’Yan Sandan jihar Yobe ta ce ta cafke wani shugaban mazaba na jam’iyyar APC a karamar hukumar Karasuwa bisa zarginsa da hannu a kisan wata mata.

Rundunar ta ce ta samu nasarar ce a binciken da take yi kan wata gawar da aka gano a kusa da Jami’ar Tarayya da ke Gashuwa a makon da ya gabata.

A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ’yan sanda daga sashin karamar hukumar Bade sun kama wani mutum mai suna Abdulmumini Garba, mai shekaru 60, dangane da mutuwar matar mai suna Falmata Abubakar, ‘yar shekara 45 da haihuwa.

Rahoton ya nuna cewa wanda ake zargin mazaunin Gasma ne a karamar hukumar Karasuwa, kuma yana rike da mukamai biyu: Sakataren APC na Mazava a Karasuwa da Sakataren Kasuwar Gwari a Gashuwa.

‘Yan sanda sun ce an kama Garba ne bayan gudanar da bincike mai zurfi da kuma kokarin leƙen asiri da suka yi a ranar 17 ga watan Oktoba, 2025.

Lokacin da ake masa tambayoyi, Garba ya amsa cewa shi ne ya kashe Falmata Abubakar a cikin motarsa, bayan samun sabani tsakaninsu.

An bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga bukatar marigayiyar na neman taimakon kuɗi don tallafa wa sana’arta, wanda ya rikide zuwa tashin hankali da ya haifar da mutuwarta.

Bayan mutuwar, wanda ake zargin ya ce ya jefar da gawar a daji da ke kusa da wajen da misalin ƙarfe 10 na dare, inda daga bisani aka gano gawar.

Rundunar ’yan sanda ta bayyana wannan ci gaba a matsayin shaida ta ƙwazo da dabarun tattara bayanai da suka taimaka wajen gano wanda ake zargi cikin gaggawa.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya jinjina wa jami’an sashin Bade bisa ƙwarewa da jajircewarsu, tare da jaddada aniyar rundunar na ganin an samu adalci.

CP Ado ya tabbatar wa da jama’a cewa za a kammala bincike cikin tsanaki, sannan a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala binciken.

Post masu alaƙa

NSCDC ta rufe wani gida da ake zargin ana safarar jarirai a Legos.

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta kama wanda ake zargi da safarar Alburusai a tankin Babur

‘Iran ta buɗe wa wani jirgi wuta a mashigar Hormuz