Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi ya buƙaci al’ummar jihar su kira shi da sunansa maimakon laƙabin da ake amfani da shi na Your Excellency.”
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar da aka tare da mataimakinsa, Aminu Usman, a wurin taro na Aminu Kano Triangle, dake Dutse.
Gwamnan ya bai wa al’ummar jihar tabbacin tafiyar da gwamnatinsa cikin gaskiya da riƙon amana tare da mutunta kowa da kowa.
Sannan ya yi kira ga sauran jam’iyyun adawa da su zo domin a haɗa kai a ciyar da jihar gaba.
Domin gwamnan ya sha alwashin tabbatar da ya cika alƙawurin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe da ya yi kafin ƙarewar wa’adin mulkinsa na farko.
Ya kuma tabbatar da cewa haɓaka tattalin arziƙin jihar na ɗaya daga cikin abubuwan da zai mai da hankali a kansu domin ganin an jawo hankalin masu zuba hannun jari wajen samar da ayyukan yi a jihar.
Sannan ya gwamnan ya ƙara jaddada alƙawarinsa na haɓaka ɓangaren lafiya da ilimi da fannin noma da kuma muhalli.
Ya kuma tabbatar da yana sane da ƙalubale na ambaliyar ruwa da jihar ta fuskanta a shekarar 2022, inda aka samu rushewar gidaje da gadoji da ma asarar rayuka masu yawa.
Inda ya yi alƙawarin kula da muhalli domin kauce wa afkuwar irin waccen hasara da aka samu.
A ƙarshe ya yaba wa gwamnan jihar, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar, saboda samun damar halartar taron rantsar da shi da aka yi.