Gwamnan Jihar Jigawa mai barin gado, Muhammad Badaru Abubakar ya musanta zargin da ake yi masa na yi wa gwamna mai jiran gado, Malam Umar Namadi, maƙarƙashiya.
Ya bayyana zargin da cewa ba shi da tushe ballanatana makama.
Gwamna Badaru ya bayyana hakan ne a Dutse yayin ganawa da Shugaban kamfanin Gerawa Globacom, Alhaji Isa Gerawa da ya kai wa Gwamnan ziyara.
Badaru ya ce kawai wasu mutane ne da ba su da makoma a siyasar jam’iyyar APC da ta jihar jigawa suke ƙoƙarin shiga tsakani.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin manya a jam’iyyar APC da suka amince wa har suke rufe ƙofa da su ne suke komawa gefe suke cin dunduniyarsu kawai don biyan buƙatar kansu.