Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa.
Yahaya, da ya yi gwamna a 2019, ya sake lashe zaben Jihar Gombe a karo na biyu a zaben 2023.
Ya gaji gwamnan Jihar Filato mai barin gado Simon Bako Lalong a matsayin shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa.