Jami’an sojin saman Nijeriya sun isa birnin Ankara na Turkiyya don samun horo kan amfani da wasu jiragen sama kirar Turkiyya.
Ma’aikatar Sararin Samaniyar Turkiyya ce ke kera jiragen masu saukar ungulu samfurin T129 ATAK.
Kakakin rundunar sojin sama ta Nijeriya, Air Commodore Ayodele Famuyiwa ne ya sanar da wannan labari.
A bara ne gwamnatin Nijeriya ta shiga yarjejeniya da Turkiyya don kerawa da samar da jirage shida samfurin T129 masu saukar angulu. Nijeriya na bukatar jiragen ne saboda yakar ‘yan ta’adda da suka addabi kasar.
Jiragen masu saukar angulu na T129 ATAK suna da inji biyu, da kujerun matuka biyu.
Kuma jiragen yaki ne da ake amfani da su wajen ayyuka daban-daban, sannan suna iya aiki a kowane yanayin samaniya.