Gwamnan jihar Sakkwato ya amince da biyan ma’aikata albashin watan Yuni da kudin fansho

Gwamnan jihar Sokoto  Ahmed Aliyu ya amince da biyan albashin watan Yuni nan take ga ma’aikatan jihar da kananan hukumomi da kuma malamai kazalika da yan fansho.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa  dauke da  sa hannun mai magana da yawun gwamnan jihar Sokoto Malam Abubakar Bawa

Sanarwar tace wannan yunkurin dai nada manufar ganin ma’aikatan jiha sun samu sukunin gudanar da sallah Babba a cikin walwala.

Gwamnan  ya kara jaddada aniyar gwamnatin sa na ganin ta kyautatawa ma’aikata tare Kuma da farfadowa da darajar aikin gwamnati. Haka kuma, ya bukaci ma’aikatan dasu sakawa wannan yunkurin ta hanyar zamowa masu gaskiya,tsare aiki da kuma zuwa aiki cikin lokaci

Gwamna ahmad Aliyu ya kuma roki alummar jihar Sokoto dasu ci gaba da yiwa Gwamnati addua don samun nasarar biyan bukatun jama’a

Post masu alaƙa

Gwamnati ta buƙaci jama’a su guji taɓa kumfar da ta ɓulla a hanyar Kaduna-Abuja

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kwace kadarorin Godwin Emefiele

Dalibai huɗu za su wakilci Najeriya a gasar Spelling Bee ta Duniya a China