Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya kafa kwamiti da zai yi duba da kuma ƙwato kadaron jihar a faɗin Najeriya.
An ɗora wa kwamitin alhakin bincikowa da kuma gano kadarori a jihar Kaduna da ofishin jihar ta Taraba da ke Legas da kuma Abuja, babban birnin Tarayya.
A cewar sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar Gebon Kataps ya fitar , ya ce an ɗora wa kwamitin nauyin nema da kuma gano inda kowane irin nau’in kadarorin gwamnatin suke a faɗin ƙasar nan.
Ya ce kwamitin zai kuma duba ƙimar kuɗin kowace kadara da kuma bai wa gwamnatin jihar shawarwari.
Ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa cikin makonni huɗu.