Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga hukumar kula da kafafen yaɗa labarai a Najeriya NBC ta da fara kula da ayyukan kafofin rediyo da talabijin na intanet.
Gwamnan ya ce sanya ido kan abubuwan da kafofin suke yaɗawa a intanet zai taimaka wajen daƙile yaɗa labaran bogi da ma abubuwan da za su iya tayar da zaune tsaye.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Mustapha Muhammad ya fitar daga cikin tsakuren jawabin da gwamnan ya gabatar a taron ƙara wa juna sani da Hukumar NBC ta shirya a jihar Legas.
A jawabinsa, gwamnan wanda ya samu wakilcin darakta-janar harkokin watsa labarai da hulɗa da jama’a, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya nuna takaicinsa kan yadda ake abin da aka ga dama a amfani da intanet wajen yaɗa abubuwan da ba su dace, “wajen yaɗa abubuwan da suke jawo rarrabuwar kai musamman na addini da siyasa. Yanzu saboda rashin sa ido, intanet ya zama wajen baje-kolin labaran bogi da kalaman ɓatanci.”
Ya ce lokaci ya yi da NBC za ta fara kula da ayyukan kafofin da suke yaɗa labarai ta intanet domin tsabtace abubuwan da suke yaɗawa.