Gwamnati ta tilasta yi wa ɗaliban sakandare gwajin ƙwaya a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bijiro da wasu sabbi kuma tsauraran matakai na yaƙi da ta’ama’li da miyagun ƙwayoyi a makarantun sakandare ciki har da tilasta yi wa ɗalibai gwajin ƙwaya da kuma dakatar da waɗanda aka gano sun ci gaba da shan ƙwaya bayan gyaran halin da aka yi masu.

A ƙarƙashin sabon tsarin, za a riƙa yi wa duk sabbin ɗalibai a makarantun sakandare gwajin ƙwaya.

Matakin na ƙunshe cikin wata takarda da ta bayyana wasu jerin matakai da aka ɗauka kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi a makarantun sakandare da ke Najeriya kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cewar takardar, an bijiro da tsarin domin samar da yanayi mai kyau na koyarwa da koyo a makarantu ta hanyar rage mummunan tasirin da ta’amali da miyagun ƙwayoyi ke yi kan lafiyar ƙwaƙwalwa da ƙwazon ɗalibai.

Post masu alaƙa

Dangote, Habasha da Djibouti za su gina bututun mai na dala miliyan 600

Sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa na haifar da sakamako mai kyau – Shettima

Kotu ta soke takarar gwamna da Pantami ke yi a Gombe