SDP ta zaɓi Farfesa Sadiq Gombe a matsayin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa

Farfesa Sadiq Umar Abubakar Gombe ya zama sabon Shugaban Jam’iyyar SDP na Ƙasa.

An sanar da zaɓensa tare da sauran mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) a ranar Asabar yayin babban taron jam’iyyar na ƙasa na shekarar 2026 da aka gudanar a Filin Wasa na Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi.

Sauran shugabannin da aka zaɓa sun haɗa da Dakta Olu Agunloye a matsayin Sakataren Jam’iyya na Ƙasa; Sanata Dokta Ugochukwu Uba a matsayin Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa mai kula da Shiyyar Kudu; Hajiya Mariam Maggie Batube a matsayin Ma’ajiya ta Ƙasa; da Barista Joseph Achille Abu a matsayin Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa.

 

Post masu alaƙa

Kwastam ta kama harsasai 3,300 da kayayyakin fasa-ƙwauri a Seme

Jigawa na da ƙarfin samar da sama da kashi 50 cikin 100 na buƙatar shinkafar Najeriya – Shugaban NUJ

Ba na tsoron duk wata barazana daga Gwamnatin Tarayya a yayin zaɓen Osun — Gwamna Adeleke