Tinubu ya isa Kenya don halartar taron ƙoli na Afirka da Faransa

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya isa Nairobi, babban birnin Kenya gabanin taron ƙoli na Afirka da Faransa da za a shafe yini biyu ana yi.

Shugaba Tinubu ya samu tarba daga jami’i a gwamnatin Kenya, Musalia Mudavadi wanda kuma shi ne sakataren da ke kula da harkokin da suka shafi ƙasashen ƙetare.

Akwai kuma Ministar harkokin waje ta Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu da Jakadan Kenya a Najeriya, Amb. Isaac Parashina.

Taron zai ƙara ƙarfafa ƙudirin Najeriya na zurfafa alaƙa da kuma haɗin kai da sauran ƙasashen Afirka da kuma Faransa.

Post masu alaƙa

Kwastam ta kama harsasai 3,300 da kayayyakin fasa-ƙwauri a Seme

Jigawa na da ƙarfin samar da sama da kashi 50 cikin 100 na buƙatar shinkafar Najeriya – Shugaban NUJ

Ba na tsoron duk wata barazana daga Gwamnatin Tarayya a yayin zaɓen Osun — Gwamna Adeleke