Gwamnatin Edo Ta Yi Allah-wadai Da Kisan ‘Yan Arewa

Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya yi Allah-wadai da kashe wasu matafiya ‘yan Arewacin Najeriya da aka yi a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar arewa maso gabashin Esan a ranar Alhamis da ta gabata, wato 27 ga Maris, inda ya bayyana kisan a matsayin na dabbanci.

Ana ta dai yaɗa wasu faya-fayan bidiyo, wanda a ciki aka nuna wasu matasa sun zagaye wasu mutane da ake tunanin mafarauta ne ƴan arewa da suka taso daga kudancin ƙasar za su koma gida wataƙila domin bikin sallah.

A wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan jihar, Fred Itua ya fitar, ya ce, “Binciken farko-farko ya nuna cewa matafiya ne da suka taso daga Fatakwal na jihar Rivers suka ratso ta garin, sai ƴan banga suka kama su da tunanin cewa ɓatagri ne.”

Post masu alaƙa

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

Zaɓen 2027: Rundunar yan sanda jihar Kano ta ba da tabbacin tsaro,tare da yin gargaɗi kan yada labaran ƙarya