Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa gwamnatin jihar, ta gano ma’aikatan bogi 6,348, yayin tantance ma’aikatan ta.
Ƙididdigar da aka gudanar ta tabbatar da cewa, ma’aikatan bogin na laƙume sama da Naira miliyan 314 a wata yayin da ake asarar kimanin Naira biliyan 3.7 a shekara a kansu.
Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwar da kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa ya fitar a ranar Talata a Dutse, babban birnin jihar.
- ‘Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Daba 24 Da Muggan Makamai A Kano
- ’Yan Bindiga Sun Harbe Malamin Jami’a Sun Sace Motarsa
Sagir Musa ya ce an gano ma’aikatan bogin ne bayan tantancewar da gwamnatin ta gudanar ta hanyar daukar hoton yatsun ɗaukacin ma’aikatan jihar.
“A yayin gudanar da wannan bincike, an gano ma’aikata 6,348 na bogi, wanda hakan ya rage wa gwamnati asarar Naira 314,657,342 a wata da kuma kusan Naira biliyan 3.7 a shekara,”