Home » GWAMNATIN JIGAWA ZA TA FARA WANKIN ƘODA KYAUTA

GWAMNATIN JIGAWA ZA TA FARA WANKIN ƘODA KYAUTA

by Hassan Abdu Mai Bulawus
0 comment
Gwmnan Jihar Jigawa, Umar Namadi Dan Modi

Gwamnatin Jigawa ta sha alwashin ɗaukar nauyin wanke ƙodar duk wani ɗan jihar da ke ɗauke da ciwon ƙodar da ke buƙatar wankewa.

Wannan ya zo ne a cikin wani bayani da Kwamishinan Lafiya na jihar Jigawa Dokta Abdullahi Muhammad Kainuwa ya yi wa abokin aikinmu Hassan Abdu Mai Bulawus, a yayin wani taro da Kungiyar Likitoci ta Ƙasa reshen jihar Jigawa ta shirya, na wuni uku a garin Hadejia, don wayar da kan mutane a kan lafiyar ƙoda ta hanyar kafofin sadarwa na zamani.

Kwamishinan Lafiyar na Jigawa wanda ya kasance Shugaban taron, ya bayyana yadda Gwamnatin ta damu a kan halin da masu buƙatar wankin ƙodar ke ciki, inda ya ce a yanzu sun tattara bayanan mutane 91 da za a fara yi musu wankin ƙodar kyauta.

“Mai girma gwamna Malam Umar Namadi ya ce ya fara gyara cibiyar wankin ƙoda ta Hadejia, a yanzu an kashe Naira miliyan 189, an kawo injin wankin, an yi bohol na samar da ruwa, an kawo janereta, Kuma mai girma Gwamna zai buɗe nan ba da daɗewa ba.”

Dokta Abdullahi Muhammad Kainuwa ya ƙara da cewa “An fara gina wasu cibiyoyin wankin ƙodar a asibitin Dutse da Rimgim da Kazaure. Kuma Mai Girma Gwamna ya ce tace ƙoda kyauta ne, ba sai mutum ya biya ko kwabo ba”.

Kwamishinan lafiyar na Jigawa ya kuma ce Gwamnan ya ba da umarnin bai wa masu ciwon suga da hawan jini magani kyauta sakamakon alaƙar cutukan da ciwon na ƙoda.

A nasa ɓangaren Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa reshen jihar Jigawa, Dokta Haruna Usman ya ce yawaitar masu fama da ciwon ƙoda ne a jihar Jigawa ne ya ja hankalinsu suka shirya taron.

A yayin taron dai masana daga asibitoci da makarantu daban-daban ne suka gabatar da takardu a kan ciwon na ƙoda, inda gwamnatin jihar ta sha alwashin ɗaukar nauyin bincike-bincikensu domin samar da mafita

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?