Gwamnatin Jihar Gwambe ta sanar da yin karin albashin naira dubu goma-goma ga ma’aikatan gwamnatin fadin jihar domin rage radadin rayuwa bayan cire tallafin mai.
Da ya ke ganawa da ƴan jarida a jiya Juma’a, mataimakin gwamnan jihar, Dokta Manassah Daniel Jatau, ya ce, wannan wani bangare ne na matakan da gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ke dauka na rage wa ma’aikata matsatsin tattalin arziki da ake ciki.
A cewarsa, wannan karin albashi na dubu goma-goma zai shafi dukkanin ma’aikatan gwamnatin jiha da na kananan hukumomi.mataimakin gwamnan, yace daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka har da raba tallafin naira dubu talatin-talatin ga mutane 420 000 a sassan jihar daban-daban.
Jatau ya kuma roki ma’aikatan jihar da su cigaba da kasancewa masu biyayya ga doka da oda, kuma ya yi kira ga al’umma musamman wadanda har yanzu ba su samu tallafi ba da su kara hakuri, kaso na nan zuwa kansu, sannan ya bayar da tabbacin cewa za su cigaba da kawo tsare-tsaren da kowa zai mora.