Gwamnatin jihar Kano ta karyata rade-radin da ake cewa ta dauki mataki akan sababbin masarautu.
Sakataren yada labarai na gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin-Tofa shine ya bayyana hakan, inda ya ce, har yanzu babu wani mataki da gwamnati ta dauka akansu.
Sunusi Bature ya ce, ba za su boye duk wani abu ba tsakanin bangaren gwamnati da majalisa ba domin bawa al’ummar jihar Kano damar sanin abinda yake faruwa akan matakan da gwamnati take dauka.
Da safiyar ranar Talata ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nemi sahallewar majalisar na daukar mutum 20 a matsayin masu bashi shawara, kuma tuni majisar ta amince a zaman da tayi na farko.
Ana saran a sati mai zuwa gwamnan jihar Kano zai tura sunayen kwamishinoni zuwa majalisa domin tantancewa.