Hukumar tsaron farin kaya ta kasa (DSS) ta gayyaci dakataccen shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annanti ta EFCC, Abdurrasheed Bawa domin amsa tambayoyi bayan da shugaba Tinubu ya dakatr da shi a yammacin jiya.
Bawa ya isa hedikwatar hukumar ta DSS da ke Abuja ‘don amsa gayyatar da aka yi masa.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Mista Peter Afunanya shi ya tabbatar da gayyatar da aka yi wa Bawa, ya kuma jaddada cewa, yana daga cikin hanyoyin gudanar da bincike kan dimbin zarge-zargen aikata ba daidai ba da ake yi wa Bawa.
Wannan lamari na zuwa ne ‘yan sa’o’i kalilan bayan da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da Abdulrasheed Bawa daga mukaminsa na shugaban hukumar ta yaki da ta’annanti ta (EFCC).
A bisa umarnin shugaba Tinubu, an umurci Bawa ya gaggauta mika ayyukan ofishinsa ga daraktan ayyuka a hukumar.
Wannan tsari zai bada damar ci gaba da aiki a ofishin shugaban hukumar har sai an kammala bincike.
Hukumar ta EFCC dai, tana taka muhimmiyar rawa wajen kare muradun kudaden kasa da kuma tabbatar da cewa an magance laifukan tattalin arziki yadda ya kamata.