Home » Waye Abba Kabir Yusuf, Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano?

Waye Abba Kabir Yusuf, Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano?

by Anas Dansalma
0 comment

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.

Muryar sanar da sakamakon zaɓen gwamna na 2023 na jihar Kano

Abba Kabir, wanda ake yi wa da laƙabi da Abba Gida-gida ya samu nasara ne a kan abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC mai mulki Nasiru Yusuf Gawuna, mataimakin gwmnan jihar Kano.

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan Kano Farfesa Dikko Ahmad Ibrahim ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Yusuf Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705.

Sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar PDP ce ta zo ta uku, inda Sadik Wali ya samu ƙuri’u 15,957, sai kuma Sha’aban Ibrahim Sharaɗa na jam’iyyar ADP ya samu ƙuri’u 9,402.

A shekarar 2019 ne Abba Kabir ya fara takarar gwamnan kano inda ya yi takara da Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC.

Jam’iyyar NNPP ce ta lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka yi  a ranar 25 ga watan Fabrairu, ta kuma lashe biyu cikin uku na kujerun sanatocin Kano, sannan da mafi yawancin kujerun majalisar wakilai daga jihar ta Kano.

An haife  Abba Kabir Yusuf a ranar 5 ga watan January,  a shekarar 1963 a ƙaramar hukumar Gaya ta nan jihar Kano.

Ya yi karatun Firamare a makarantar gwamnati da ke Sumaila Primary School sannan kuma ya yi karatun Sakandire a makarantar gwamnati ta Lautai a Gumel da ke jihar Jigawa.

Abba ya yi karatun difloma a kwalejin kimiya da fasaha ta Mubi sai kuma babbar difloma a kwalejin kimiya da fasaha ta Kaduna watau Kaduna Polytechnic.

Ya yi karatun digirinsa na biyu a jam’iyyar Bayero ta Kano a fannin harkokin kasuwanci.

 Kuma shi yayi Tsohon kwamishinan ayyuka a jihar Kano a zamanin mulkin Rabi’u Musa Kwankwaso.

Abba gida-gida ya yi takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kano a shekarar 2019 amma bai samu nasara ba.

Yana da mata biyu da ‘ya’ya da dama.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?