Mako guda bayan hukumar kula da gidajen yarin Najeriya ta bayyana cewa babu ɓullar cutar kwalara a cibiyoyinta da ke fadin kasar nan, kwamishinan lafiya na jihar Legas ya bayyana cewa an samu mutum 25 da suka kamu da kwalara a gidan yari na Kirkiri da ke jihar.
Darakatan yada labarai na ma’aikatar lafiya ta jihar Legas, Tunbosun Ogunbanwo ne ya bayyana hakan in da ya ce, kawo yanzu mutane 25 ne suka koka kan mummunan ciwon ciki.
- Gwamnatin Borno Ta Ce ‘Yan Boko Haram Ne Suka Kai Hari Goza
- Najeriya Sabon Jini Take Buƙata ~ Obasanjo
Sanarwar ta ce, an ɗauki matakin gaggawa wajen shawo kan lamarin.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya ta ce mutum 53 ne suka mutu a watan Yunin 2024 sanadiyyar yaɗuwar cutar a faɗin ƙasar.