Gwamnatin jihar Borno ta dora alhakin harin kunar bakin wake da aka kai kan masu daurin aure a garin Gwoza kan mayakan Boko Haram.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Borno, Usman Tar, ya shaida wa manema labarai cewa kungiyar masu tada kayar baya ta Boko Haram ce ta kai harin.
Ya ce ‘yan ta’addar sun kai wannan hari ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke shirin mayar da mazauna yankunan gidajensu da ke gudun hijira a halin yanzu.
- Mutum 4 Sun Mutu Yayin Binne Mataimakin Shugaban Malawi Saulus Chilima.
- Sadaukarwa ce za ta sa mu cimma burinmu ~ Tajuddeen Abbas
Gwamnatin jihar ta ce, tana shirin rufe sansanin ‘yan gudun hijira da ke jihar baki daya daga nan zuwa shekarar 2026.
Usman Tar ya ce harin na ranar asabar din karshen makon da ya gabata da ya hallaka mutune 18 bai musu dadi ba.