Gwamnatin Kamaru ta tabbatar da cewa mutum hudu suka mutu a zanga-zangar da ƴanƙasar suka gudanar a ranar Lahadi a birnin Doula gabanin sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a yau Litinin.
Ɗaruruwan magoya bayan ɗantakarar adawa, Issa Tchiroma Bakari ne suka fito zanga-zangar.
Hukumomi sun ce an kai wa ƴansanda da jami’an tsaro hari ne, dalilin da ya sa suka kare kansu.
Tchiroma Bakary ya ƙalubalanci shugaba Paul Biya – wanda ya shafe shekara 43 yana shugabanci a ƙasar.
Tuni jagoran adawar ya ayyana cewa shi ne ya yi nasara a zaɓen, duk da cewa a yau Litinin ne ake sa ran sanar da sakamakon a hukumance.