Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar 29 ga wannan wata na Maris da kuma 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun Good Friday da Easter Monday.
Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka a madadin Gwamnatin Tarayya a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Aishatu N’dayako.
Tunji-ojo ya yi amfani da wannan damar ya yi kira ga mabiya addinin Kirista da ma ƴan ƙasa baki ɗaya su yi koyi da karantarwa Yesu Almasihu kamar yadda ya nuna a rayuwarsa.