Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Sabon Shugaban Gidan Gyaran Hali Ya Mayar Da Hankali Wajen Gyara Tarbiyar Daurarru

Daga : Shareep Khaleepha Sharifai

 

Gwamnatin tarayya ta bukaci sabon shugaban hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali na kasar Sylvester Nwakuchi, da ya mayar da hankali wajen sauya tunanin  daurarru maimakon hukunta su kawai.

Ministan harkokin cikin gida Dr. Olubunmi Tunji Ojo ne ya yi wannan kira yayin bikin nadin da aka yi wa sabon shugaban hukumar a birnin tarayya  Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A jawabinsa, ministan ya jaddada muhimmancin shugabanci na gari ta hanyar rikon gaskiya da amana wajen kawo sauyi mai inganci a tsarin gidajen ajiya da gyaran hali, tare da dora wa sabon shugaban alhakin tabbatar da sauyi cikin watanni 19 masu zuwa.

A nasa bangaren, Sylvester Nwakuchi ya yi godiya da sabon mukamin naa tare da bayyana shirin sa na inganta tsaro, rage cinkoso, samar da gine gine da kuma walwalar ma’aikata.

Post masu alaƙa

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

Zaɓen 2027: Rundunar yan sanda jihar Kano ta ba da tabbacin tsaro,tare da yin gargaɗi kan yada labaran ƙarya