Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Kwamitin Tsara Jigilar ‘Yan Najeriya Daga Sudan

Wata sanarwa da Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta kasa NEMA ta fitar dauke da sa hannun kakakinta, Manzo Ezekiel,ita  ta bayyana kafa kwamitin kamar yadda Channels ya ruwaito.

Kasashen Birtaniya, China, Amurka Saudiyya da sauran kasashen duniya na ta yunkurin ganin yadda za su kwashe ‘yan kasarsu.

A ranar Asabar Saudiyya ta yi nasarar kwashe mutum 50.

A makon da ya gabata ne, kasar ta Sudan da ke Arewacin Afirka ta tsunduma cikin rikicin tsakanin dakarun kasar da wasu mayaka masu sanye da kayan sarki da ake kira RSF.

Kafa wannan kwamiti da hukumomin Najeriya suka yi, shi ne mataki na baya-bayan da kasar ta dauka, kasa da sa’a 24 bayan da gwamnati ta ce babu halin da za a yi jigilar saboda yanayi na rashin tsaro musamman a yankin filin tashin jirgin Khartoum

Sai dai a ranar Asabar NEMA ta ce kwamitin na dauke da kwararru a fannonin ba da agajin gaggawa, da kuma bincike da kubutarwa.

Hukumar ta NEMI ta kuma kara da cewa, tana ci gaba da tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki kan lamarin tare da tattara bayanan da suka dace.

Post masu alaƙa

Barista Hamza Ɗantani ya jinjinawa CP Bakori da wasu kwamishinonin yan sanda biyu.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ceto fasinjoji 9 bayan musayar wuta da yan bindiga a hanyar Doguwa.

Kwalejin Fasaha ta Kogi ta dakatar da lakcarori 7 kan cin zarafin ɗalibai