Gwamnatin tarayyar ta zargi dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar Labor, Peter Obi da cin amanar kasa tare da kuma tunzura jama’a bayan ya fadi a zabe.
Ministan Yada Labarai da Al’adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed ya yi wannan jawabin a zantawarsu da wasu manya kafafen yada labarai na duniya a birnin Washington DC.
Ministan ya ce, ba zai yiyu Obi da mataimakinsa Datti Ahmed su ci gaba da yi wa ‘yan Najeriya barazana game da rantasar da zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ba.
Ya ƙara da cewa Wannan cin amanar kasa ne.
Wannan na zuwa ne bayan bayyanar wani faifen murya wanda a cikinsa aka jiyo muryar da ake zargin ta Peter Obi ce, yake bayyana zaben 2023 a matsayi yaki na addini.