Gwamnatin Jihar Yobe, ta kammala gina da gyaran kasuwanni bakwai na zamani tare da masana’antun sarrafa iri huɗu, a wani yunƙuri na bunƙasa kasuwanci da samar da ayyukan yi a jihar.
Kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu, Yawon Buɗe Ido da Ma’adinai na jihar, Kaigama Yusufari, ne ya bayyana hakan yayin taron tattaunawa da manema labarai a Damaturu.
Ya ce kasuwannin da aka kammala suna Potiskum, Damaturu, Geidam, Nguru, Gashuwa, Yunusari da Ngalda.
A cewarsa, aikin gina kasuwanni a Machina, Buni Yadi da Buni Gari ya kai matakan kammalawa, kuma ana sa ran miƙa su ga ma’aikatar a watan Disamba.
Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnati ta amince da gina ƙarin kasuwanni a Yusufari, Baymari, Sabon Garin Nangere, Girgir, Ngelzerma, Bumsa da Babbangida.
Ya ce shirin gwamnatin Mai Mala Buni shi ne gina kasuwa ta zamani a kowace daga cikin ƙananan hukumomi 17 na jihar.
Ana shirin farfaɗo da masana’antu
Yusufari ya ce an kammala masana’antun sarrafa iri huɗu a Machina, Nguru, Potiskum da Damaturu, inda ake jiran buɗe su.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta ɗauki matakan farfaɗo da wasu masana’antun da suka daɗe ba sa aiki, ciki har da Sahel Aluminum Industry da ke Potiskum, masana’antar sarrafa garin fulawa da abincin dabbobi, da ke Potiskum, masana’antar siminti ta Pre-pressed da ke Damaturu, da masana’antar ƙera buhunan leda.
Haka kuma, gwamnati ta amince da farfaɗo da kamfanin ruwan roba na Dofarga Spring Water da ke Gulani, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen farfaɗo da kamfanin haɗa takin zamani na Gujba.
Kwamishinan ya ce wani kamfani daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya nuna sha’awar saka hannun jari a masana’antar sarrafa irin ridi ta Potiskum.
Ya ƙara da cewa an riga an sanya hannu kan yarjejeniya, kuma ana jiran kammala sauran matakai.
An kammala aikin filin ajiye manyan motoci
Yusufari ya ce an kammala aikin filin ajiye manyan motocin dakon kaya a Potiskum, yayin da ayyukan katafariyar kasuwar zamani da tashar mota ta zamani a Damaturu suka kai matakan kammalawa.
Ya kuma bayyana cewa jihar na da ma’adinai 26 da ba a fara amfani da su ba, inda ma’aikatar ta ɗauki mai ba da shawara domin tantance wuraren da suke, yawansu da ingancinsu.
Yobe na shirin bunƙasa yawon buɗe ido
A ɓangaren yawon buɗe ido, kwamishinan ya ce jihar na shirin karɓar baƙuncin gasar tseren motoci da raƙuma a hamada, bisa tsarin wasu gasanni da ake gudanarwa a Dubai da Gabas ta Tsakiya.
Ya kuma ce ana shirin farfaɗo da bikin kamun kifi na Bade, tare da bunƙasa bukukuwan al’adu na Machina da Gudi Hill domin jawo baƙi da ƙara samun kuɗaɗen shiga a jihar.