Za mu kashe duk wanda ya yi yinƙurin maguɗi a zaɓen 2027 – Omo-Agege

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege, ya yi barazanar kashe duk wanda ya yi yunƙurin tafka maguɗi a zaɓen shekarar 2027.

Omo-Agege, wanda ke neman kujerar Sanatan Delta ta Tsakiya a jam’iyyar NDC, ya yi wannan barazanar ne a wani taron siyasa.

“Duk wanda ya yi maguɗin zaɓe a ranar zaɓe, za mu kashe shi,” in ji shi.

A baya, Omo-Agege ya tsaya takarar gwamnan Jihar Delta a ƙarƙashin jam’iyyar APC, amma ya sha kaye a hannun Gwamna Sheriff Oborevwori na jam’iyyar PDP.

Bayan Oborevwori ya sauya sheƙa zuwa APC, Omo-Agege ya nemi tikitin jam’iyyar domin komawa Majalisar Dattawa, amma Sanata David Dafinone mai ci a yanzu ya kayar da shi a zaɓen fid-da-gwani.

Daga bisani, Omo-Agege ya koma jam’iyyar NDC, inda ya sha alwashin kayar da Dafinone a zaɓe mai zuwa.

A watan Mayu, Omo-Agege ya ce ya yanke shawarar komawa NDC ne bayan tuntuɓar magoya bayansa.

Ya bayyana cewa yana ganin jam’iyyar za ta ba shi damar yi wa al’ummar Delta ta Tsakiya da Najeriya hidima yadda ya kamata.

Post masu alaƙa

Cutar Ebola da aka gano a Najeriya na kama da wadda ta ɓarke a Kenya

An sanya wa’adin kammala sabuwar tashar lantarki a Katsina

Gwamnatin Yobe ta kammala gina kasuwanni 7 da masana’antu 8, ta shirya garfaɗo da wasu