Gwamnonin Najeriya na duba yiwuwar mayar da mafi karancin albashi N100,000

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana cewa gwamnoni na nazarin yiwuwar ɗaga mafi ƙarancin albashin ƙasa zuwa Naira 100,000, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

AbdulRazaq ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce hauhawar farashi, tsadar rayuwa da matsin tattalin arziƙi da ma’aikata ke fuskanta ne suka sa ake duba batun.

Ya ce gwamnatocin jihohi na tattaunawa da gwamnatin tarayya da kuma ƙungiyoyin ƙwadago domin cimma matsaya kan sabon tsarin albashi da zai inganta rayuwar ma’aikata tare da tabbatar da cewa jihohi za su iya ɗaukar nauyin biyan albashin.

A cewarsa, manufar ita ce ƙara ƙarfin sayen kayan masarufi na ma’aikata tare da bai wa gwamnatoci damar ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da hidimomin jama’a.

A halin yanzu, mafi ƙarancin albashi a Najeriya na tsaye ne a kan naira 70,000 a wata, yayin da wasu jihohi ke biyan fiye da hakan.

Post masu alaƙa

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.