Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta bayyana jin daɗinta tare da miƙa godiya ga dukkan waɗanda suka taka rawa wajen tabbatar da gudanar da bukukuwan Babbar Sallah ta shekarar 2026 cikin kwanciyar hankali da lumana a sassan jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar kuma ya rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce rundunar ta yaba wa gwamnatin jihar bisa gudunmawar da ta bayar, da shawarwari da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, lamarin da ya taimaka wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a lokacin bukukuwan.
Hakazalika, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa al’ummar jihar kan haɗin kai da goyon bayan da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
CP Bakori ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da aiki tuƙuru domin hana duk wani abu da ka iya haifar da fitina ko tayar da hankalin jama’a, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da kai rahoton duk wani abu da suke zargin zai iya zama barazana ga tsaro cikin gaggawa ga jami’an tsaro, domin ɗaukar matakin da ya dace