Home » Ba A Ɗage Dokar Haramta Wa Ƴan Najeriya Biza Ba

Ba A Ɗage Dokar Haramta Wa Ƴan Najeriya Biza Ba

by Halima Djimrao
0 comment

Haɗaɗɗiyar Daular Ƙasashen Larabawa ta ƙaryata iƙirarin da gwamnatin Najeriya tayi cewa ta janye dokarta da ta haramta bai wa ƴan Najeriya  bizar shiga ƙasar.

Wani jami’in gwamnatin ƙasar ta Daular Larabawa ya shaida wa wani gidan yaɗa labarai na wata ƙasar waje cewa har yanzu babu wani canji game da maganar biza tsakanin ƙasashen biyu. Jami’in ya buƙaci a ɓoye sunansa saboda ya yi magana da ƴan jarida ba da izini ba.

A watan Oktoban shekarar 2022 Haɗaɗɗiyar Daular Ƙasashen Larabawa ta faɗa a cikin wata sanarwa cewa ba za ta ƙara bai wa ƴan ƙasar Najeriya biza ba tare da ƴan wasu ƙasashen Afirka 19.  

A baya cikin sauƙi ake iya samun bizar yawon shaƙatawa da buɗe ido ta tsawon wata ɗaya kafin Haɗaɗɗiyar Daular Ƙasashen Larabawan ta daina bai wa ƴan Najeriya biza haka kwatsam.

Tun bara aka dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin ƙasashen biyu bayan matakin da kamfanin jiragen saman Emirates na Dubai ya ɗauka na daina zuwa Najeriya saboda wasu kuɗaɗensa da yace sun maƙale a Najeriya.

Kamfanin jiragen saman Haɗaɗɗiyar Daular Ƙasashen Larabawa na Emirates ya ce kuɗaɗensa har dola miliyan 85 sun kasa fita daga Najeriya. 

A makon jiya ne shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da Sarkin Haɗaɗɗiyar Daular Ƙasashen Larabawa Mohamed bin Zayed Al Nahyan Al-Thani a Abu Dhabi inda shugabannin biyu suka daddale wata yarjejeniya ta tarihi kamar yadda wata sanarwar gwamnatin Najeriya ta faɗa.

A cikin sanarwar, gwamnatin Najeriya ta ce yarjejeniyar ta share hanyar ɗage dokar haramta bizar,  kuma nan take za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin ƙasashen biyu.

Bugu da ƙari kuma wai daga ƙulla yarjejeniyar ta tarihi nan take kamfanonin jiragen saman Etihad da Emirates za su ci gaba da zirga zirga daga ciki da wajen  Najeriya, a cewar sanarwar ta gwamnatin Najeriya.

Sai dai kuma a wata sanarwar da gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Ƙasashen Larabawan ta fitar daga bisani, ta ce shugabannin ƙasashen biyu sun tattauna ne kawai don duba hanyoyin yiwuwar samar da ƙarin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu da fatan ƙarfafa hulɗa tsakaninsu, amma babu maganar ɗage haramcin biza ko kuma ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin ƙasashen biyu.

A cikin wata sanarwar ƙarin bayani daga mai bai wa shugaban Najeriya shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya ce jami’an gwamnatocin ƙasashen biyu suna buƙatar ƙarin lokaci su daddale bayanan dake cikin yarjejeniyar, sai dai wannan sanarwar ta saɓa wa wadda ya fitar tun da farko.

Ngelale ya ce ganin yadda shugabannin ƙasashen biyu suka ƙulla yarjejeniyar, akwai buƙatar a bada dama ga jami’an gwamnatocin biyu su tattauna da kyau kafin su daddale yarjejeniyoyin da suka shafi fannoni da dama, ya ƙara da cewa, ya kamata yanzu kowa ya bar matakin ya yi aiki,  ba shisshigi, ba inda-inda,  kuma ba tare da jita-jita ba.

An yi murna sosai lokacin da aka ce an ɗage dokar da ta haramta bayar da bizar saboda Dubai wuri ne da dubban yan Najeriya masu shaƙatawa da buɗe ido ke matuƙar son zuwa, kuma wuri ne na zuba jari ga yan Najeriya masu harkokin gine-ginen gidajen sayarwa.

Kafin annobar cutar korona, ƴan Najeriya na cikin manyan masu zuba jari a Dubai cikin harkokin gine-ginen gidajen sayarwa, ƴan Najeriya sun zuba jarin da ya kai kusan dola miliyan dubu biyu a harkar a cewar wasu rahotannin kafafen yaɗa labaran Dubai da suka ruwaito bayanai daga ma’aikatar kula da filayen ƙasar.

Kuma kafin a dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin ƙasashen biyu,  jiragen Emirates na tashi sau biyu a rana daga Lagos zuwa Dubai, da kuma sau ɗaya kullum daga birnin Abuja zuwa Dubai.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi