Hana Ɗangote Mai A Naira Ya Tashi Farashinsa A Najeriya

@Alhaji Musa Yahaya Mai Kifi,

Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewacin ƙasar.

Sabon tsarin daina sayar wa matatar Dangote mai a farashin Naira ya fara aiki ne a ranar 28 ga watan Maris, 2025.

Wannan ya sa gidajen mai suka ƙara farashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a Legas, da Naira 940 a yankin Kudu maso Yamma da Kwara, sannan Naira 960 a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas

Rahotanni sun nuna cewa farashin ya fi ƙaruwa a Arewa, yayin da Legas ke da mafi ƙarancin farashi.

Kamfanin MRS Oil & Gas na jigilar mai daga Legas zuwa sassa daban-daban na ƙasar.

Duk da haka, ba a bayyana takamaiman wajen da aka sayo sabon man fetur ba, amma yanzu ana sayar da shi a farashin da ya bambanta da na baya.

 

 

 

Post masu alaƙa

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC