Home » Hanyoyin kare Kai Daga Kamuwa Daga Cutar koda

Hanyoyin kare Kai Daga Kamuwa Daga Cutar koda

Likita ya ce hawan jini da ciwon suga na cikin cututtukan da ke haddasa ciwon koda - ya kamata mutum ya dinga kokarin zuwa asibiti don a ba shi magungunan da suka dace da kuma kula da ciwonsa na hawan jini ko ciwon sugari don kare shi daga kamuwa da ciwon koda.

by Zubaidah Abubakar Ahmad
0 comment

Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa cutar hawan jini da suga na cikin cututtukan da ke haddasa ciwon koda – ya kamata mutum ya dinga kokarin zuwa asibiti don a ba shi magungunan da suka dace da kuma kula da ciwonsa na hawan jini ko ciwon sukari don kare kaii daga kamuwa da ciwon koda.

Alamomin ciwon koda kamar yadda likitoci suka bayyana sun hada da kumburi da yawan kasala da fitsari mai kumfa da yawan amai har zuwa jijjiga.

Dr Mujahid sanusi likitan koda daga asibitin malam Aminu Kano ya yi bayani kan hanyoyin kare kai daga kamuwa da ciwon koda Ya ce kariya daga kamuwa da ciwon ba wani abu ba ne mai wahala ko tsada domin ba abubuwa ne masu girma ba da za a ce ba za a iya yi ba.

Ya ce mutane za su iya kare kansu daga kamuwa da cutar koda ta hanyar cin abinci mai gina jiki da kuma kiyaye duk abubuwan da aka ce suna janyo cutar.

Amma duk wanda ya samu ciwon koda zai sha wahala ta tsadar magunguna da sauran matakai na waraka. Matakan kariya sun hada da:

Ana son mutum ya kiyaye magungun da yake sha, ya kare kansa da shan magungunan da ba a san sahihancinsu ba, da suka shafi na gargajiya da shan na Bature da ya wuce kima. Likita ya ce shan wasu magunguna na bature fiye da kima na haifar da ciwon koda.

Sannan ya ce ya kamata duk maganin da mutum zai sha ya kasance ya nemi shawarar likita domin kiyaye lafiyar koda.

Duk lokacin da mutum ya samu rashin lafiya ko da zazabi ne, ya kamata ya yi kokarin zuwa asibiti domin tabbatar da ya samu kulawar da ta dace ta kwararrun likita don samun maganin da ba zai taba masa koda ba.

Likita ya ce hawan jini da ciwon suga na cikin cututtukan da ke haddasa ciwon koda – ya kamata mutum ya dinga kokarin zuwa asibiti don a ba shi magungunan da suka dace da kuma kula da ciwonsa na hawan jini ko ciwon sugari don kare shi daga kamuwa da ciwon koda.

Zuwa asibiti, a cewar liktita zai taimaka duba duk wasu abubuwa da za su kawo ciwon koda domin a magance su da wuri ba tare da an kai yanayin da kodar ta mutu gaba daya ba ta aiki a jiki ba.

Ana son mutum ya yawaita shan ruwa, likitoci na bada shawarar shan ruwa akalla gora uku wato lita uku a rana daga safe zuwa washegari.

Rashin shan isasshen ruwa a lokacin gumi kan janyo ciwon koda.

Yawan shan ruwa zai sa mutum ya samu isasshen ruwa a jikinsa kuma jini yana zuwa kodarsa don ta yi aiki sosai.

Cin gishiri da yawa yana cikin abubuwan da ke janyo hawan jini, likitoci na bada shawarar rage yawan cin gishi domin idan ya yi yawa a jiki yakan taba koda. Motsa jiki hanya ce ta waraka daga cuttuka da za su kare koda.

Likita ya bada shawarar a dinga motsa jiki domin zai taimakawa wajen magance hawan jini da ciwon suga tare da kare koda.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?