Harin Borno: Shettima Ya Ziyarci Maiduguri, Ya Jajanta Wa Sojoji

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ziyarci Maiduguri a ranar Asabar domin jajanta wa Rundunar Sojin Najeriya da gwamnatin Jihar Borno kan hare-haren da aka kai wa sojoji.

An kai hare-haren ne a Benisheikh, Ngamdu da Pulka, inda aƙalla sojoji 18 suka rasu, tare da wasu fararen hula.

Shettima, ya ce ya kai ziyarar ne bisa umarnin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu.

Ya yaba da jajircewar sojojin wajen kare ƙasa, yana mai cewa bai kamata a manta da irin sadaukarwar da suka yi ba.

A yayin ziyarar, ya gana da manyan hafsoshin soji da jami’an gwamnati da ke kula da ayyukan tsaro a yankin.

Manyan jami’an gwamnati da na tsaro ne suka tarbe shi.

Shettima, ya ce rasuwar sojojin abin takaici ne ga ɗaukacin ƙasa, yana mai cewa ƙoƙarinsu na taimakawa wajen kare al’umma duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tallafa wa sojoji da iyalan waɗanda abin ya shafa.

Ya ƙara da cewa gwamnati na da ƙudirin inganta tsaro da kuma tabbatar da cewa masu aikata laifi ba za su tsira ba.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda