An kammala tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran

Tawagar manyan jamai’an Iran da Amurka sun yi zaman tattaunawar sulhu ta sa’o’i biyu a birnin Islamabad.

Ba a sanar da matsayar zaman ba, amma wakilin BBC ya ce amincewar bangarorin biyu su yi ganawar kai tsaye alama ce ta nasara.

Kafar yaɗa labaran Iran ta ce za a ƙara wata tattaunawar a ƙarshen mako.

Wakilan Amurka ba su ce komai ba game da zaman tattaunawar sulhun.

Ɓangarorin biyu na zargin juna da karya yarjejejniyar tsagaita wuta.

Ya yinda suke neman matsaya game da batutuwa da dama da suka haɗa da wucewa ta mashigin Hormuz da janyewa Iran takunkumai da tabbatar da tsagaita wuta a Lebanon da kuma makomar shirin nukiliyar Tehran.

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai