Harin Iran a Isra’ila ya jikkata mutum 14

Rahotanni daga hukumomin Isra’ila sun ce wani hari da Iran ta kai da makami mai linzami a Tel Aviv a yau ya jikkata mutum 14.

Ba a samu rahoton cewa harin ya lalata wurare ba lalacewa amma hukumomin agajin gaggawa na Isra’ila sun ce mutum goma sha huɗu sun jikkata sakamakon hare-haren a unguwannin da ke kusa da Tel Aviv.

A safiyar yau, an yi kira ga mazauna wasu yankuna a tsakiyar Isra’ila, ciki har da Tel Aviv, su nemi mafaka sau da dama.

Hukumomin Isra’ila sun ce mutum 19 ne suka mutu tun farkon rikicin, mafi yawansu sakamakon ƙananan ɓirɓishin makaman masu linzami da aka kakkaɓo

Post masu alaƙa

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC