Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya sanya hannu kan sabuwar doka da za ta ninka tsawon hukuncin ɗauri zuwa 10 ga wanda aka samu da alaƙar auren jinsi a ƙasar.
Sabuwar dokar, wadda majalisar dokoki ta ƙasa ta amince da ita a ranar 11 ga Maris, 2026, ta sake fasalin gabatar da ƙara yawan abin da tsohuwar dokar ta ƙunsa.
Sashe na 319 na dokar a yanzu ya bayyana cewa dokar ta ƙunshi “duk wata alaƙar jima’i ko yunƙurin jima’i tsakanin mutum biyu masu jinsi iri ɗaya, haɗi da yunƙurin jima’i da gawa ko dabba.
Dokar wadda ta kasance ɗaya daga cikin alƙawuran yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar, Bassirou Diomaye Faye da Firayim Minista Ousmane Sonko, an aike da ita zuwa majalisar dokokin ƙasar bayan da aka kama wasu da ake zargin suna da alaƙar jinsi ɗaya, wadda tuni aka haramta ta a ƙarƙashin dokar Senegal.
A shekarun bayan-bayan nan wasu ƙasashen Afirka sun gabatar da dokoki masu tsauri kan alaƙar jinsi ɗaya.
A watan Satumban shekarar da ta gabata ne majalisar rikon kwarya ta Burkina Faso ta amince da kudirin dokar haramta yin alaƙar jinsi a ƙasar, bayan makwabciyarta Mali a shekarar 2024.
Haka ma a 2023, Uganda ta amince da wasu tsauraran dokokin haramta auren jinsi a ƙasar, inda za a iya yanke wa mutumin da aka samu da laifin hukuncin ɗaurin rai da rai.