Harsashi daga wurin biki ya yi ajalin wata budurwa mai shekaru 14 a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Wata budurwa ‘yar shekara 14 ta rasa rayuwata bayan wani harsashi da ake kyautata zaton an harbo shi daga wurin bikin aure a tsallako gidansu da ke rukunin gidajen ma’aikatan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri a ranar Asabar.
Da farko dai an ce bikin na sojoji ne, amma daga bisani babban kwamandan rundunar Operation Haɗin Kai da ke yaƙi da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ya musanta zargin, inda ya ce jami’an sa kai ne suke bikin aure.
Ya yi gargaɗi cewa mutane su riƙa kula kafin su yaɗa labarai, domin gudun yaɗa ƙarya ba gaira ba dalili.
Tuni dai aka fara bincike kan gaskiyar abin da ya faru domin ɗaukar matakin faruwar hakan a nan gaba.
Wata majiya da ba’a bayyana sunanta ba ta ce budurwar sun gama yin lalle ke nan da mahaifiyarta a lokacin da mummunan al’amarin ya faru.
An yi jana’izar ta a jiya Lahadi a Maiduguri babban birnin jihar Borno kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Post masu alaƙa

Ƴan sandan Kano za su ƙara ƙaimi wajen amsa kiran gaggawa – CP Bakori

Masu Garkuwa Da Janar Rabe Na Neman A Sako ’Yan Bindigar Da Ke Hannun Gwamnati

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu