Hastsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 12 Edo

Aƙalla fasinjoji 12 ne suka ƙone ƙurmus a wani mummunan hatsari da ya auku a kan titin Benin zuwa Auchi a Jihar Edo.

Kakakin Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a Edo, Cyril Mathew, ya tabbatar da aukuwar hatsarin.

Ya ce wata mota ƙirar Toyota Hiace ce ta yi karo da babbar tifa.

A cewarsa, hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na asuba a ranar Asabar, a kusa da wani shingen sojoji da ke yankin Igueoviobo.

“Motar ta taso ne daga Zuba a Babban Birnin Tarayya tana kan hanyarta n zuwa Benin, amma ta yi karo da wata babbar tifa da ke kan hanyar zuwa Auchi.

“Duk fasinjojin da ke cikin motar sun rasa rayukansu,” in ji shi.

Mathew, ya ce ana zargin direban motar da gajiya yayin tuƙi, lamarin da ya sa ya fara barci a kan hanya, wanda hakan ya haddasa hatsarin.

Karon da motocin suka yi ya haddasa tashin wuta, lamarin da ya sanya fasinjojin zuka ƙone ƙurmus.

Sai dai direban babbar tifar da yaronsa sun tsira ba tare da sun ji rauni ba.

Kakakin ya shawarci direbobi da suke hutawa a duk lokacin da suka gaji domin gujewa aukuwar hatsari.

Post masu alaƙa

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda

‘Talauci ya faɗo daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto