Daga: Suraj Na’Iya Idris Kududdufawa
Wasu iyayen yara a karamar hukumar Fagge sun yi zanga-zangar kin jinin sabuwar shugabar makarantar sakandiren GGASS Tudun Bojuwa.
An hango iyayen yaran sun cika filin makarantar ne suna nuna rashin goyon bayansu akan sabuwar shugabar makarantar da aka kawo musu.
Iyayen yaran sun bayyana cewar akwai sabuwar shugabar makaranta (principal) da aka kawo musu da ake kiranta da suna Hajiya, wadda dududu satin ta hudu da kawowa, amma ta kawomusu ci gaban da a shekaru hudu baya ba a kawomusu ba.
- NLC Za Ta Fara Zanga-zanga Ranar 4 Ga Fabarairun 2025
- ECOWAS Ta Bayyana Matsayarta Kan Nijar, Mali Da Burkina Faso
Iyayen yaran sun kara da cewar hatta tarbiyyar yaransu ta sauya sosai gashi kuma yaran suna matukar gane karatu da mai da kai.
Yayin tattaunawar tashar MUHASA da shugaban iyayen yara na makarantar ta GGASS Tudun Bojuwa ya bayyana cewa, kwatsam sai su kaji mummunan labarin za a dauke wannan mata a kawomusu wata wadda basu yarda da ita ba, domin sun gudanar da bincike akan wadda za a kawo sun ce tana da wasu kudire kudire marasa kyau da aka taba korar ta a makarantu guda biyu a Kano a matsayinta na shugabar makaranta.
Sun ce, makarantun da aka taba korar wadda suke kin jinin kawota sun hadar da makarantar sakandire ta shinge da kuma ta barikin sojoji.
Daga karshe an hango iyayen yaran sun kafe kwalaye sannan sun daga wasu a hannayensu suna nuna kin jinin wannan sauyi a ake nema ayi musu.
Sai dai kawo lokacin hada wannan rahoto bamu samu jin ta bakin hukumar ilimi ta karamar hukumar Fagge ba.