Hisba ta kama mutane 7 dake musayar matansu na aure

Hukumar Hisba a shiyyar Katagum ta jihar Bauchi ta yi nasarar kama wasu mutane bakwai da ake zargi da aikata wani sabon salo na musayar mata domin hulɗar aure da jima’i a tsakanin su, a Azare cikin ƙaramar hukumar Katagum.

Bayanan hakan ya fito ne daga bakin Kwamandan Hisba na shiyyar Katagum, Malam Ridwan Muhammad Khairan yayin zantawa da manema labarai a garin Azare, inda ya ce an cafke mutanen ne bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga al’umma da wasu daga cikin ’yan ƙungiyar da ake kira “Wuddadu”.

A cewar Malam Ridwan “An kama waɗannan mutane ne bisa zargin shiga wata yarjejeniya inda suke musayar matansu domin hulɗar aure da jima’i a tsakaninsu.”

Kwamandan ya ƙara da cewa, wannan ɗabi’a ba ta da tushe a addinin musulunci, yana mai cewa: “Wannan aiki babu wata hujja a shari’ar Musulunci da ke goyon bayansa, duk da cewa wasu daga cikinsu sun yi ƙoƙarin jingina shi da mafarki da ɗaya daga cikinsu wai ya ce ya yi.”

Kwamandan na Hisba ya jaddada cewa, Hisba ba za ta lamunci duk wani abu da ya saɓa wa koyarwar addini da ɗabi’un al’umma ba, yana mai gargaɗin cewa za su ɗauki matakin doka kan duk wanda aka samu da aikata irin wannan aiki da ke da alaƙa da baɗala.

Ya ce: “A ƙarƙashin shari’ar Musulunci, dole ne aure ya kasance an yi shi bisa ƙa’ida tare da shaidu, kuma abin da waɗannan mutane suka aikata ya yi kama da zina kai tsaye.”

A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar ta Wuddadu a Azare da ke ƙaramar hukumar Katagum, Malam Sagir Bashir ya ce sun shafe sama da shekara guda suna ƙoƙarin gyara halayen waɗanda abin ya shafa ta hanyar nasiha da jan kunne.

Ya ce: “Mun yi ƙoƙari sosai wajen hana wannan ɗabi’a ta hanyar gargaɗi da ba su shawara, amma suna ci gaba da aikatawa a ɓoye, wanda hakan ya tilasta mana kai rahoto ga Hisba domin kare mutuncin al’umma.”

Ya kuma bayyana cewa irin wannan abu ya taɓa faruwa a baya, inda aka gargaɗi waɗanda suke aikata laifin tare da alƙawarin daina wa, amma daga baya suka koma yin hakan.

A cewarsa: “Wannan ɗabi’a ba ta cikin koyarwar addininmu, illa wasu daga cikinsu da suka yi iƙirarin cewa suna samun mafarki da ke goyon bayan hakan.”

Post masu alaƙa

Zauren haɗin kan malamai ya buƙaci gwamnatin Kano ta tsawatarwa ƴan daba da masu saka su.

NNPCL ya ƙulla yarjejeniyar gyara matatun man fetur na Warri da Fatakwal

Juyin mulki: Mutum 2 sun amince sun san da shirin kifar da gwamnati