Home » Hukumar Hizba ta fara rabon fom ɗin auren zawarawa da ‘yan mata a jihar Kano

Hukumar Hizba ta fara rabon fom ɗin auren zawarawa da ‘yan mata a jihar Kano

by Anas Dansalma
0 comment
Hukumar Hizba ta fara rabon fom ɗin auren zawarawa da 'yan mata a jihar Kano

KANO:

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta ce ta kafa kwamitoci guda biyu waɗanda za su yi aikin rabon fom da tantance lafiyar masu buƙatar shiga shirinta na auren zawarawa da ‘yan mata.

Ta ce shirye-shiryen sun yi nisa, tun bayan samun amincewar gwamnatin Kano na gudanar da shirin auren zawarawa da ‘yan mata 1,800.

Shugaban Hizba ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce za a bai wa ƙananan hukumomin cikin birnin Kano takwas, gurbin mutum hamsin kowacce, yayin da ƙananan hukumomin wajen birni kuma za a ba su gurbin mutum 30.

Fitaccen malamin ya ce idan mutum yana da sha’awar shiga shirin, da farko zai je ya karɓi fom. Sannan a cike bayanai muhimmai da hukumar Hizba take buƙata guda shida.

“Na farko”, in ji Sheikh Daurawa, “mu san asalin mutum. Na biyu mu san sana’arsa, mu san halayensa, sannan mu tantance lafiyarsa.”

Sannan mai nema zai ya kawo mutanen da za su ba da shaida a kansa cewa (shi) mutumin kirki ne.

Kuma a samu cikakken bayani dangane da inda yake  da zama

Ya ce hukumarsu ba haɗa auren za ta yi ba, ga duk mai sha’awar shiga shirin zai karɓi fom ne bayan ya/ta daidaita da wanda yake/take son auren.

BBCHAUSA                                                             AM/AS           

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?