Hukumar Kashe Gobara ta ƙasa reshen jihar Kaduna ta gargadi mazauna jihar saboda yuwuwar samun gobara a lokacin sauyin da ake dab da shiga.
Kwamandan hukumar, Sadiq Usman, wanda ya bayyana hakan a matsayin wani mataki na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya ce ya zama dole a yi wannan gargaɗi idan aka yi la’akari da yadda ake cigaba da fuskantar matsalar sauyin yanayi.
Kuma a lokutan sanyi, al’umma na ninƙa yadda suke amfani da na’urori ko ma kunna wuta domin ɗumama ɗakunansu wanda hakan ke yawan haifar da gobara.
Inda ya ce suna wannan kira ne domin sauke nauyin da ke kansu wajen hana afkuwar gobara a lokacin sanyi.