• Home  
  • Hukumar NOA ta buƙaci al’umma su haɗa kai domin yaƙar laifukan ta’addanci
- Babban Labari

Hukumar NOA ta buƙaci al’umma su haɗa kai domin yaƙar laifukan ta’addanci

Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa, wato NOA, ta yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su hada kai wajen yakar ta’addanci da sauran matsalolin tsaron da ke fuskantar kasar nan, inda tace mabanbantan yaruka da addinan da Najeriya ke da shi wata babbar ni’ima ce. Sai dai hukumar tace hakan bai kamata a […]

Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa, wato NOA, ta yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su hada kai wajen yakar ta’addanci da sauran matsalolin tsaron da ke fuskantar kasar nan, inda tace mabanbantan yaruka da addinan da Najeriya ke da shi wata babbar ni’ima ce.
Sai dai hukumar tace hakan bai kamata a bari masu aikata laifuka su rika yin amfani da hakan wajen haddasa matsalolin tsoro da rarrabuwar kawuna ko rashin zaman lafiya a kasar ba.
Babban Daraktan Hukumar, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana hakan bayan nasarar da jami’an tsaron kasar nan suka samu ta kubutar da dalibai da malamai da wasu da ake zargin masu Garkuwar da mutane ne suka yi garkuwa da su a wasu makarantu da ke karamar hukumar Orire a Jihar Oyo.
Mallam Lanre ya kuma yabawa jami’an tsaron kasar bisa jarumtaka da nuna kwarewa gami da sadaukarwar da suka nuna, harma ya bayyana hakan a matsayin babbar nasarar dake sake tabbatar da muhimmancin hadin gwiwa da amfani da ingantattun bayanan sirri wajen yaki da miyagun laifuka

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000