Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce shugabancin Nijeriya na daya daga cikin kalubale mafi tsanani a rayuwa da mutum zai samu kansa a ciki.
Buhari ya bayyana hakan ne a jiya a cikin sakonsa na barka da Sallah mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, inda ya jaddada cewa shugabanci na bukatar hadin kai da goyon bayan dukkan ‘yan kasa.
Buhari ya kuma yi wa Musulman Nijeriya barka da Sallah tare da yi wa wadanda suka yi aikin Hajji fatan yin ibada karbabbiya da kuma dawowa gida lafiya.