Hukumar Tennis ta Duniya ta dakatar da Quentin Folliot.

A wata sanarwa da hukumar ta ITIA ta fitar ta ce ta gano ɗan was an, ɗan asalin ƙasar Faransa ya aikata laifuka 27 da suka danganci cin hanci da rashawa, waɗanda sun saɓawa shirin yaƙi da rashawa na hukumar kula da wasannin Tennis ta Duniya.

Baya ga dakatarwar an kuma ci tarar ɗan wasa Folliot, mai shekaru 26, zunzurutun kuɗi har dalar Amurka dubu 70, kwatankwacin Yuro dubu 52, yayin da aka kuma umarce shi da ya mayar da wasu kuɗaɗe da ya yi almundahanar su waɗanda suka kai sama da dalar Amurka dubu 44, kwatankwacin Yuro dubu 33 kenan.

Wannan hukunci dai na nufin hana ɗan wasan yin wasanni, ko koyar da wasan, ko kuma halartar duk wani wurin da ake buga wasan tennis.

Dama dai tun a ranar 17 ga watan Mayun bara ne aka dakatar da ɗan wasan na wucin gadi, saboda haka a yanzu zai ci gaba da zama cikin wannan haramci har zuwa ranar 16 ga Mayun 2044, wanda a lokacin zai cika shekaru 45 da haihuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *