ICPC ta ce zata binciki zargin cin hanci da Dangote ke yi wa Shugaban NMDPRA

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (ICPC) ta ce za ta fara bincike nan take kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai na  Kasa (NMDPRA), Farouk Ahmed.

Hukumar ta bayyana cewa haka ne a yayin da sanar cewa ta karɓi takardar korafin da Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya shigar kan Farouk Ahmed.

Mai magana da yawun hukumar ICPC, John Odey, ya bayyana cewa za a gudanar da cikakken bincike kan korafin. A ranar Talata ne attajirin ɗan kasuwar, ta hannun lauyansa, ya shigar da korafi yana neman a kama tare da gurfanar da Shugaban na NMDPRA.

Dangote ya zargi Farouk Ahmed da cin hanci da rashawa da kuma amfani da karfin ofishinsa wajen almundahana da karkatar da kudaden gwamnati domin amfanin kansa, wanda hakan ke cutar da al’ummar Nijeriya.

Lauyansa, Dakta Ogwu Onoja, SAN, ya rubuta wasikar zuwa ICPC a madadinsa, ya ce yana da kwararan hujjoji da ke goyon bayan zarge-zargen da yake yi wa Ahmed.

Dangote ya fara yin zargin ne a ranar Lahadi, a taron manema labarai da ya gudanar a Legas, inda ya zargi shugabancin NMDPRA karkashin Ahmed da dakile ayyukan matatun mai na cikin gida, ta hanyar ci gaba da bayar da lasisin shigo da kayayyakin mai daga waje, “duk da karuwar karfin tace mai a cikin gida.”

A cewarsa, shigo da man daga kasashen waje na hana bunkasar masana’antu a cikin gida, tare da samar da ayyukan yi a kasashen waje, yayin da ‘yan Nijeriya ke fama da matsalar masana’antu.

Daga bisani, Majalisar Wakilai ta kasa ta shiga tsakani a rikicin, inda ta gayyaci Dangote da Ahmed domin nemo hanyar warware matsalar.

Sai dai duk da shiga tsakani da ’yan majalisar suka yi, Dangote ya bukaci ICPC da ta binciki Ahmed tare da gurfanar da shi, domin hakan ya zama darasi ga sauran mutanen da ake zargin suna yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa.

Da yake mayar da martani ta cikin wata gajeriyar sanarwa, Odey ya ce: “Hukumar ICPC na sanar da jama’a cewa ta karɓi wata wasikar korafi a hukumance a yau Talata, 16 ga Disamba, 2025, daga Alhaji Aliko Dangote ta hannun lauyansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *