Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya ta ce ta kama likitan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke tsare a wajenta saboda saɓa ƙa’idojin duba lafiyarsa da kotu ta bayar.
Hukumar ta ce ta kama Farfesa Bello Abubakar, bisa zarginsa ba da bayanan ƙarya a yayin da ake bincike.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, John Odey, ya fitar, ICPC El-Rufai ya ƙi amincewa ya halarci zaman kotun da ya kamata a gudanar a Kaduna a ranar 6 da 7 da 8 ga watan Yuni, inda ya nace sai an haɗa shi da likitansa.
Sakamakon hakan ne hukumar ta ce ta ce ta amince da duba lafiyar tsohon gwamnan kamar yadda kotu ta yi umarni.
Hukumar ta ƙara da cewa kamar yadda iyalansa suka buƙata, jami’anta sun fita daga ɗakin a lokacin duba shi a babban asibitin ƙasa domin mutunta sirrinsa.
Sai dai ICPC ta ce daga bisani ta gano wasu hotuna da wani abokin siyasar El-Rufai, Isa Ashiru Kudan, ya wallafa a shafinsa na Facebook, waɗanda ke nuna tsohon gwamnan tare da wasu baƙi, ciki har da likitansa, a lokacin da aka ware domin duba lafiyarsa.
Hukumar ta ce hakan ya nuna cewa an yi amfani da damar ziyarar jinya wajen yin wasu abubuwan da ba su cikin abin da kotu ta amince da shi.
ICPC ta kuma ce za ta sanar da kotu abin da ta kira saɓa wa umarninta da aka yi.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da tsare Farfesa Bello Abubakar domin ci gaba da bincike kan zargin da ake masa.