Majalisar Dattawan Najeriya na so a daina yi wa tubabbun Boko Haram afuwa

Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin gyaran hali da sake haɗa tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’umma.

Majalisar ta cimma wannan matsaya ne a zamanta na ranar Talata, sakamakon ci gaba da sace-sace da kashe jami’an soji da ƴanbindiga ke yi a ƙasar.

Shugaban kwamitin majalisar kan rundunar sojin Najeriya, Sanata Abdulaziz Yar’Adua, mai wakiltar Katsina ta tsakiya ne ya fara gabatar da ƙudurin kan abubuwan da ke faruwa na rasin tsaro a ƙasar.

Ya ce hare-hare da sace-sace da kashe jami’an tsaro masu aiki da kuma waɗanda suka yi ritaya na ƙaruwa, musamman Manjo Janar Rabe Abubakar da ya mutu a hannun ƴanbindiga a makonnin da suka gabata.

Bayan gabatar da ƙudurin ne kuma Sanata Joseph Ikpea daga Edo ta tsakiya ya buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin yi musu afuwa da maida su cikin al’umma.

Da yake goyon bayan ƙudurin, Sanata Adams Oshiomhole, mai wakiltar Edo ta Arewa, ya ce, “Hankali ba zai ɗauka ba, a ce ana yi wa masu aikata laifuka afuwa sannan a sake yi musu gyaran hali. Saboda haka ina goyon baya.”

Daga bisani majalisar ta kaɗa ƙuri’ar amincewa da buƙatar inda ta umarci kwamitocinta masu kula da harkokin tsaro su ƙara sa ido kan ayyukan hukumomin tsaro tare da tabbatar da cewa suna ɗaukar matakan da suka dace wajen shawo kan matsalolin a ƙasar.

Post masu alaƙa

APC ta nada Abdulaziz Yari a matsayin jagoran kamfen na Tinubu

Zan mayar da tallafin man fetur idan na ci zaɓe – Atiku

Gwamnonin da ke shirin murɗe zaɓen 2027 za su sha mamaki — Kwankwaso