Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙara mafi ƙarancin kuɗin fansho daga Naira 12,000 zuwa Naira 20,000 a kowane wata ga tsofaffin ma’aikatan gwamnati da na ƙananan hukumomin jihar.
A cewar Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Sagir Musa Ahmed, gwamnatin za ta kashe sama da Naira biliyan biyu a duk shekara domin aiwatar da sabon tsarin biyan fanshon.
Majalisar ta kuma umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), da ta gaggauta kai kayan agaji ga yankunan da guguwa ta shafa a jihar, tare da ci gaba da tantance asarar da aka yi.
A fannin kiwon lafiya kuwa, gwamnatin ta amince da kashe Naira biliyan biyu da miliyan 136 domin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a manyan asibitoci huɗu da ke Birnin Kudu, Ringim, Kazaure da Bulangu.
Haka kuma, Majalisar ta amince da kashe Naira biliyan uku da miliyan 340 domin aiwatar da shirin bunƙasa samar da madara a jihar.
Ana sa ran shirin zai inganta harkokin kiwo, samar da ayyukan yi da kuma ƙara yawan madarar da ake samarwa.
Bugu da ƙari, gwamnatin ta ware naira miliyan 923 da dubu 670 domin ci gaba da shirin tallafa wa ma’aikatan gwamnati a noman daminar bana, domin bunƙasa samar da abinci da ƙara musu hanyoyin samun kuɗin shiga.
A ɓangaren ilimi kuma, an amince da kashe sama da Naira miliyan 581 domin sayen motocin aiki da kwamfutoci ga hukumomin ilimi domin inganta gudanar da ayyukansu.
Gaba ɗaya, gwamnatin ta amince da kashe sama da Naira biliyan tara kan waɗannan shirye-shirye da suka shafi walwalar ‘yan fansho, kiwon lafiya, noma, kiwo, ilimi da kuma agajin gaggawa ga waɗanda iftila’i ya ya shafa.