Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana zaben gwamnan jihar Adamawa a matsayin wanda bai kammala ba, watau “Inconclusive.”
Jami’in hukumar ta INEC wanda ke da alhakin tattara sakamakon zabe a jihar ya ce adadin katin zabe na dindindin da mutane suka karba a yankunan da aka samu matsala 37,000 ya zarce tazarar da ke tsakani.
A cewarsa, adadin ya zarce tazarar da ke tsakanin gwamna Ahmadu Fintiri na PDP da babbar abokiyar karawarsa, Sanata Aishatu Binani, ta jam’iyyar APC, kamar yadda majiyarmu ta rawaito.